Yawan kudaden da ake asara wurin bayar da cin hanci ya haura dala tiriliyan daya. Ana kuma yin asarar kimanin dala tiriliyan 2.6 ta hanyar zamba a kowce shekara, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Yau ce ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar ne domin wayar da kai game da illolin cin hanci da almundahana da kuma kira da a yaki matsalolin.
Kudaden da ake asara ta wadannan hanoyoyi sun kai kashi biyar na arzikin da ake samarwa a kasashe. Adadin ya kai ninki goma na kudaden tallafin da ake bayarwa ga kasashe masu tasowa.
Baya ga kasancewarsu manyan laifuka da ke iya gurgunta gwamnatoci ko hana su samar da ayyukan ci gaba yadda ya kamata, cin hanci da zamba na iya durkusar da masana’antu da harkokin kasuwanci.
Gwamnatoci da kasashe da ke fama da wadannan matsaoli sun dauki matakai daban-daban domin yakar cin hanci da rashawa.
Kowacce akwai irin matakan da ta dauka da kuma ikirarin da take yi game da nasarorin da take samu a wannan bangare.
Su kuma jama’a ra’ayoyinsu sun bambanta game da salon yaki da cin hanci da rashawa.
Sun bayyana haka ne a shafuknmu na sada zumunta, inda muka tambaye su yadda suke kallon yaki da rashawa da cin hanci, musamman a kasashe kamar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wasu daga cikin masu sharhi na cewa haka ba ta cimma ruwa ba a yaki da rashawar.
Daga cikinsu kuma akwai masu zargin hukumomi da bin son zuciya ko yin amfani da yaki da cin hanci da rashawa a matsayin makamin siyasa a kan ‘yan adawa.
Ahmad Sulaiman Bajoga ya ce “SO HANA GANIN LAIFI! Yaki da cin hanci da rashawa dai a Najeriya abu ne da yazamo na bangaranci. Idan kana gefena kai wankakke ne”.