
Hakkin mallakar hoto
@GovKaduna
Gwamnoni sun ce dokar ta saɓawa kundin tsarin mulki
Batun ba majalisar dokoki da ɓangaren shari’a a jihohi ‘ƴancin cin gashin kai a Najeriya na neman tayar da ƙura tsakanin shugaban ƙasa da kuma gwamnoni.
A ranar 22 ga watan Mayu ne Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wata doka da ake kira Executive Order 10 da ta ba ƴan majalisar dokoki da kotuna ƴancin cin gashin kai.
Shugaban kuma ya umarci ofishin babban akanta na ƙasar da ya cire wa duk jihar da ta ci gaba da rike wa majalisar dokoki da bangaren shari’a kuɗin da ta rike daga kasonta na wata.
Sai dai kuma gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun nuna rashin amincewa da dokar da shugaba Buhari ya sanya wa hannu, inda suka ce ƙudirin ya saɓa wa sashe na 121 na kundin tsarin mulki na 1999.
Dokar na nufin za a ware wa majalisun dokoki na jiha da ɓangaren shari’a kudadensu a kasafin kuɗi, inda za su yi wa kansu kasafin kuɗi kan dukkanin abubuwan da suke buƙata, matakin da gwamnoni ba sa so.
Bayan wani taro da suka yi kan batun ranar Juma’ar da ta gabata, gwamnonin sun cimma matsayar ƙalubalantar matakin kuma rahotanni sun ce shugaban ƙungiyar gwamnonin – Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti – ya gana da Buhari da kuma ministan shara’a kan batun.
Ƙungiyoyin ƙwadago da ‘ƴan Najeriya da dama sun yaba da matakin shugaban ƙasar na amincewa da dokar wadda ake ganin za ta ba ƴan majalisar dokokin jiha ƴanci waɗanda ake ganin sun koma ƴan amshin shatan gwamnonin duk da ƙarfin da kundin tsarin mulki ya ba ƴan majalisar jihar.
Yanzu duk kuɗaɗen da gwamnatocin jihohi suka karɓa daga kason asusun Gwamnatin Tarayya ko abin da suke samu na kuɗaɗen shiga dole su raba wa sauran ɓangarorin gwamnati nasu kason.
Kuma dokar ta ba Babban Akanta na Ƙasa damar zare kuɗaɗen duk jihar da gwamnanta ya ƙi cire wa ɓangaren majalisar dokoki da shari’a nasu kason.
Dokar dai na son daidaita ƙarfin da kundin tsarin mulki ya ba ko wane ɓangare na gwamnati a matakin jiha, musamman duba da ƙarfin da gwamnoni ke da shi a Najeriya.
Tun kafa jamhuriyya ta huɗu ake ganin gwamnoni sun ƙara wa kansu ƙarfin da ke danne sauran ɓangarorin gwamnati, duk da ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba su.
Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau
Gwamnoni na iya garzayawa kotu domin ƙalubalantar dokar
Dokar na nufin tabbatar da ƴanci ga majalisar jiha tare da yin duba ga ayyukan zartarwa da kuma ɗora alhakin ci gaban al’umma ga gwamnati.
Kudirin dokar shugaban da ya ba ƴan majalisar dokoki da ɓangaren jihohi cin gashin kai ya samo asali ne tun daga majalisa ta 8, inda shugaban ƙasar daga baya ya kafa kwamiti da ya ba shi shawarwarin aiwatar da shi.
Majalisar ta yi gyara ne ga kundin tsarin mulki na Najeriya, inda aka ba majalisar dokoki da ɓangaren shari’a na jihohi cin gashin kai, yayin da yanzu za a dinga sa kuɗaɗensu cikin kasafin kudi na jiha.
Honorabul Aminu Shehu Shagari, tsohon Shugaban Kwamitin Shari’a ne a Majalisar Wakilai kuma shi ne ya gabatar da buƙatar da ta kai ga kafa dokar kuma mamba a kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, ya shaida wa BBC cewa sun yi nazari kan dokar.
Ya ƙara da cewa sun yi hakan ne saboda yadda dimokuradiya ke tafiya a jihohi ba kamar yadda ake bukata ba.
Ya ce dimokuradiyya ba za ta tafi yadda ake so ba idan sai dukkanin ɓangarorin tafiyar da gwamnati sun dogara da gwamnati kafin iya aiwatar da duk wani abin da suke buƙata.
A cewarsa, wani muhimmin ɓangare na dokar shi ne, dukkanin ɓangarorin gwamnati za su zauna su tsara kasafin kuɗinsu, za su kuma san abin da jihar ta ke da shi da abin da babu.
“Duk abin da majalisa ta ke son ta zartar za ta yi kan duk wani abin da ƴan majalisar ke ganin al’umma za su amfana. Haka ɓangaren shari’a na jihohi zai iya yanke hukunci yadda ya kamata ba tare da wani shakku ba,” in ji shi.
Sannan ya ce yanzu ɓangarorin za su san nawa ko wane ɓangare ke kashewa musamman wajen biyan albashi da kuma kuɗaɗen alawus na ‘ƴan majlisar da masu taimaka masu da kuma kuɗaɗen kula da tafiyar da ofis.
Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau
Buhari ya ba ‘ƴan majalisar dokoki da kotuna ‘ƴancin cin gashin kai
Yanzu babu hannun gwamnonin kan abin da ƴan majalisar dokokin za su kashe, wanda hakan zai sa majalisar aiwatar da aikinta ba wani shakku.
Dokar na nufin tabbatar da ‘ƴanci ga majalisar jiha tare da yin duba ga ayyukan zartarwa da kuma ɗora alhakin ci gaban al’umma ga gwamnati.
Yadda gwamnonin suka fito suna adawa da ba majalisar dokoki da ɓangaren shari’a na jihohi cin gashin kai, ana ganin za su iya ƙalubalantar matakin a gaban kotu.
Honarabul Aminu ya ce gwamnonin na iya zuwa kotu, kuma kotu za ta iya kawo tsaiku idan ta ce a jira, kuma za a iya ɗaukar lokaci ba a cimma nasarar abin da ake son cimma wa ba.
Ya ce kamar yadda kwamitin shugaban ƙasa ya bayar da shawara, ya kamata a zauna da kowace jiha a ji ƙorafinta a shata yadda ya kamata tsakanin kakakin majalisa da kuma gwamna.