Me ya sa APC da PDP suke ce-ce-ku-ce a kan kudin Abacha? | BBC Hausa

PDP ta zargi APC da sace kudin da aka karbo a wurin Abacha a baya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PDP ta zargi APC da sace kudin da aka karbo a wurin Abacha a baya

Zargin da PDP, babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya ta yi cewa wasu shafaffu da mai na shirin wawure $311m da Amurka ta mayar wa gwamnatin Najeriya a makon nan, ya janwo ce-ce-ku-ce tsakaninta da jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Wata sanarwa da kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Laraba ta yi zargin cewa ta bankado wani shiri da “wasu shafaffu da mai da ke fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC suke yi na amfani da kwangilar bogi da kuma fakewa da yin aikin da aka taba yi da zummar sake sace $311m.”

PDP ta ce shugabannin APC da mutanen da take zargi ‘yan-korensu ne a fadar shugaban kasar sun dade tana amfani da salon da ke ikirarin son tallafa wa jama’a wajen sace $322 da a baya a mayar wa kasar, inda suka ce sun raba su ga marasa galihu a jihohi 19 na kasar.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta bukaci a bai wa majalisar dokokin tarayyar kasar kudin domin ta yi kasafinsu “domin hana wannan gwamnatin sake sace su ta hanyar yin ayyukan da aka riga aka yi.”

Sai dai a martanin APC ta yi zargin cewa PDP tana hadiyar yawu ne kawai saboda ganin zunzurutun kudin da bata isa ta sace kamar yadda take yi a baya ba.

“Mun fahimci mawuyacin halin da PDP take ciki. Yunkurinsu na shafa wa APC kashin-kaji game da cin hanci don É“ata mata suna ya gaza… Abin takaici shi ne, PDP ta kasa fitar da cin hanci daga cikin É“argonta kuma idan bata watsar da É“urÉ“ushin cin hancin da ke jikinta ba, ba za ta daina magagi kan kudaden jama’a ba,” in ji sanarwar da mai magana da yawun APC, mallam Lanre Issa-Onilu, ya fitar.

Ya kara da cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen ayyukan yi gaban ‘yan Najeriya kamar yadda aka yi a baya.

Kifi na ganinka mai jar koma

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PDP ta zargi APC da sace kudin da aka karbo a wurin Abacha a baya

Masana harkokin siyasa na ganin wannan ce-ce-ku-ce tsakanin jam’iyyun biyu wata hanya ce ta tabbatar da abin da Hausawa kan ce ‘kifi na ganinka mai jar koma’ domin kuwa zai haska fitila a kan kudaden yadda dole a yi amfani da su wajen ayyukan ci gaba.

Malam Kabiru Sai’idu Sufi, Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Kano kuma mai sharhi a kan harkokin siyasa ya shaida wa BBC cewa “zargin da PDP ta yi abu ne da ake yi na yau da kullum a siyasance, amma yana da amfani sosai; hikimar yin hakan shi ne idan ka nuna kana sa ido kan abin da abokin hamayyarka yake yi, to zai yi kokarin yin abin da ya dace.

“Ita kanta APC lokacin da take hamayya ta yi haka. Shi ya sa ma tana hawa mulki ta soma gudanar da bincike kan kudaden da take zargi an sace, inda ta rika gurfanar da mutanen da take zargi a gaban kotu,” a cewar Malam Sufi.

Ya kara da cewa a al’adance jam’iyyar da ke mulki da wadda take hamayya tamkar kyawan da É“era don haka ba sa ga-maciji da juna.

Da ma dai an dade ana fargaba game da amfani da kudaden da aka karbo daga wurin Abacha.

Ita kanta Amurka ta taɓa gargadin gwamnatin Najeriya cewa kada ta kuskura ta bari a sake sace kudin idan ba haka ba za ta gamu da fushinta.

Gwamnatin kasar dai ta sha cea tana amfani da kudin ne wurin inganta rayuwar ‘ya’yanta.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...