Me ke haifar da tsadar Shinkafa a Najeriya?

Shinkafa

Shinkafa abinci ce ga kowa ba ga gidan talaka ko mai kudi ba, domin ta kasance cimar da aka fi ci a Najeriya, sai dai da alama tana neman gagarar masu karamin karfi sakamakon yadda farashinta ke hauhawa musamman a ‘yan watannin nan.

Masu saya domin ci a gida da masu sayar da shinkafa na bayyana korafinsu kan yadda a kullum farashin ke sauyawa duk da cewa ana samun Æ™aruwar kamfanonin cikin gida da ke samar da shinkafar da kuma yadda mutane suka sake rungumar sana’ar noma.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali shi ne ƙarfafa noman shinkafa da hana shigo da ita daga ƙetare cikin ƙasar a kokarin bunƙasa noman gida da kuma sake bude kofar samun kuɗaɗen shiga.

Gwamnatin tana ikirarin cewa a yanzu manoman Najeriya na ciyar da kasar, kuma an rage kudin da ake wajen shigar da shinkafa kasar da ya kai dala miliyan a kowace rana, kamar yadda Malam Garba Shehu kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa BBC.

Sai dai hana shigo da shinkafar waje da rungumar noman gida da ake ganin zai kawo sauki da arahar abincin da alama ba wani tasiri ya ke yi ba, ganin yadda tsadar shinkafar ta sauya daga abin da aka saba gani a baya tun kafin ma a rufe iyakoki.

Yadda firashin shinkafar gida take a wasu jihohi

  • A jihohi kamar Kano ana sayar da buhun shinkafar gida tsakani dubu 22,000 zuwa 24, 000 maimakon dubu 16,000 da aka sayar a Janairu 2020.
  • A Jihar Bauchi firashin ya sauya daga 15,500 zuwa 16,000 a Janairu zuwa 21,500 zuwa 22,000
  • A Borno ana sayar da shinkafar akan 23,000 zuwa 24,500, yayinda a watan Janairu shinkafar na kan 17,500
  • A jihar Legas ana sayar da buhu tsakanin dubu 19,000 zuwa 20,500 a yanzu
  • A Kaduna firashin shinkafar a Janairu 18, 000 zuwa 19, 000 amma yanzu 22,000 zuwa 22,500

Me ya jawo hauhawar firashin?

Alhaji Aminu Ahmed shi ne mai kamfanin Tiamin Rice a Kano kuma a tattaunawarsa da BBC ya shaida cewa akwai dalilai da dama da suka haddasa tsadar shinkafar, na farko akwai karin kuÉ—i wajen sayo shanshera.

Ya ce, a baya suna siyo tan din shanshera a kan dubu 120 zuwa 125, idan ta yi tsada dubu 130, amma a yanzu tan din shanshera jiƙaƙƙiya ya koma dubu 200.

Sannan ya ce idan ka tsaftacce shinkafar ka yi lissafi kusan ka shafe dubu 220 zuwa dubu 230 kenan wajen sayo tan guda.

Ya ce a baya lokacin da ake sayan tan din shanshera a kan dubu 120 zuwa 125 ana sayar da buhun shinkafa a kan dubu 14 zuwa 16, amma da sabon firashin yanzu buhu na kai wa 19, 500 zuwa 20,000.

”Dole mu sa riba da kuÉ—in ma’aikata da kuÉ—in wuta don haka kasuwar tana tafiya ne da yanayin da ka samo shanshare wato firashinsa.”

Sai dai Alhaji Aminu ya ce, mutane sun fi raja’a ne a kan shinkafa don kuwa ba ita kaÉ—ai ba ce ta yi tsada akwai sauran hatsi danginsu masara da gero da firashinsu ya ninka sama da na shinkafar.

”Sauran hatsin da ake raina wa sun fi shinkafar tsadar, saboda su tun ba a sarrafa su ba sun ninka kudinsu, ina ga batun an sarrafa su kuma.”

Shin laifin waye?

Kusan ba za a ce ga dalilin sauyin firashin da ake samu na shinkafa ba, tun kafin a sarrafta ko a gyarata, amma tabbas ana iya alaƙanta yanayin da ake ciki da batun annobar korona da rufe iyakoki, inji Alhaji Aminu.

Ya ce, ‘yan kasuwa daga kwari sun ajiye sayar da atamfa sun koma bin gonnaki suna saye kayan amfani gona sannan su sake sayarwa kamfanoni ta yadda za su ci riba da kyau.

”Wannan na daga cikin dalilan da ake ganin sun sake haddasa tsadar kayan abinci, idan za a cire mutanen da yanzu suka kasance ‘yan tsakiya da an samu sauki sosai”

Amma a cewar Alhaji Aminu kungiyarsu ta masu harkar shinkafa na shirya tarukan Æ™ara wa juna sani da ganin yadda za a cire ‘yan tsakiya da ke taka rawa wajen tsadar kayan abinci.

Sannan ya ce tun da a bana ana hasashen samun wadatuwar albarkatun gona musamman ita shinkafar suna zuba ido don ganin idan aka yi girbi yadda wadatuwar zata kasance,

Karin bayani

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Æ™kasar ta rufe iyakokin ta da zummar daÆ™ile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunÆ™asa tattalin arziki, ko da yake ‘yan kasar da dama sun koka kan matakin.

A watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin Najeriya ta ce ‘yan kasar sun ga irin amfanin da rufe iyakokin Æ™asar ya yi a fannin tattalin arzikinta.

Sai dai ‘yan Najeriya musamman a arewacin Æ™asar na bayyana takaici kan tsadar kayan abinci wanda suka yi tunanin a baya cewa ana iya samun rangwame la’akari da tsare-tsaren gwamnatin.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...