MDD ta soki sojojin Sudan | BBC Hausa

Antonio Gutarres

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda sojoji suka karkashe tare da raunata masu zanga-zanga a Sudan.

Antonio Guterres ya yi tir da rikicin da kuma amfani da karfin da ya wuce kima da soji suka yi a kan fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkata mutane da dama.

Ya ce matakin da sojoji suka dauka na amfani da karfin tsiya a kan masu zanga-zangar na Sudan, wajen tarwatsa su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu tari abun takaici ne.

Ya ce ya ji takaici kan rahotannin cewa sojin sun bude wuta har a cikin asibiti domin murkushe masu zanga-zangar, yana mai tunasar da majalisar mulkin rikon kwarya ta sojin a kan alhakin da ya rataya a wuyanta na kare lafiya da kuma tabbatar da tsaron ‘yan kasar ta Sudan.

Mista Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da ke wannan dambarwa da su yi taka tsantsan.

Sakatare janar din ya kuma nemi hukumomin kasar ta Sudan da su tabbatar da gudanar da bincike mai zaman kansa na musabbabin kisan tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata shi.

Sannan ya yi kira ga bangarorin da su bi hanyar tattaunawa ta maslaha kan batun mika mulki ga kwamitin rikon kwarya na bisa jagorancin farar hula kamar yadda kungiyar kasashen Afrika ta AU ta bukata.

Antonio Guterres ya ce Majalisar Dinkin Duniyar a shirye take ta yi aiki tare da kungiyar ta AU wajen bada goyon bayanta ga wannan shiri, tare da bayar da goyon baya ga alummar Sudan wajen tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa a kasarsu

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...