Wata mujallar Birtaniya da ke kawo labarai dangane da lafiyar hakora ta bayyana cewa mayukan goge baki na gawayi da wasu kamfanoni ke sayarwa suke ikirarin na sa hasken hakora da kuma kare hakora daga lalacewa ba gaskiya bane.
Akasarin mayukan goge bakin na gawayi da ake sayarwa basu cika daukar sinadarin ”Fluoride” ba da ke taimaka wa wajen kare lafiyar hakora.
Mawallafan mujallar sun bayyana cewa babu wasu kwararan hujjoji da za a iya cewa za su kare ikirarin da kamfanonin ke yi na mayukan da suke sayarwa na gawayi na fitar da dauɗa da kuma saka hasken hakora.
Mujallar ta bayyana cewa yawan goge baki da mayukan zai iya yin illa ga hakoran bai wai ma ya kara masu lafiya ba.
Sun ta bayar da shawara ga mutane da su rinka zuwa wajen likitocin hakora domin samun shawarwari kan hakoransu da irin mayukan da suka da ce da su.
Sun kuma ce ya fi nagarta mutum ya ci gaba da amfani da man goge baki mai sinadarin ”fluoride.”
An fara amfani da gawayi domin tsaftace baki a tsohuwar daular Girka mai dumbin tarihi inda mazauna wannan wuri ke amfani da gawayi domin tsaftace baki don gudun makalewar abinci da kuma warin baki da sauran cututtuka da za a iya samu kamar yadda mujallar ta bayyana.
Me sanannu ke cewa?
Dakta Joseph Greenwall-Cohen na daya daga cikin mawallafan wannan mujallar wanda malami ne a cibiyar horar da likitocin hakora da ke jami’ar Manchester.
Joseph ya bayyana cewa, ”shaguna da dama sun ta sayar da nau’in mayukan goge baki na gawayi tun bayan da sannanun mutane kamar su mawaka suka fara magana kan wadannan mayukan”
Amma ya bayyana cewa abubuwan da sannanun mutanen ke cewa a ya yin tallata wadannan mayukan ba gaskiya bane tun bayan da wani rahoto da aka fitar a Amurka a 2017 ya nuna hakan bayan tantance irin wadannan kayayyakin kusan iri 50.
Wasu sun bayyana cewa mayukan na taimaka wa wajen kashe manyan cututtuka da ke addabar harshe da dasashi da kuma taimakawa wajen haskaka hakora.
Binciken da aka gudanar ya bayyana cewa mutane na goge bakinsu a kai a kai da wadannan mayukan da zummar ganin cewa za su samu sauki ta bangaren saye da kuma saurin gyaran hakora.
Amma dakta Joseph ya bayyana cewa yawan goge baki da wadannan mayukan na iya kawo matsala musamman ma ga mayukan da ba su dauke da sinadarin ”fluoride.”