Mayaƙan Iswap sun kashe mutum 13 a Borno

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayaƙan ISWAP sun kashe aƙalla mutum 13 a ƙauyuka da dama na jihar Borno.

An kai hare-haren ne a ƙauyuka huɗu, cikin kwanaki biyu.

Wasu mazauna ƙauyukan sun shaida wa wasu jaridun Najeriya cewa mayaƙan sun kuma sace mutane da dama.

More from this stream

Recomended