Mayaƙan ISWAP sun kashe manoma 40 a jihar Borno

Wasu ƴan bindiga da ake zargin mambobin ƙungiyar ƴan ta’addar ISWAP sun kashe aƙalla manoma 40 a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya rawaito cewa an kai harin ne a ranar Lahadi.

Bayanai da ya fitar sun bayyana cewa manoman sun  cimma yarjejeniyar inda suka  biya haraji ga wani tsagin kungiyar ta ISWAP da zai ba su damar isa gonakinsu dake kusa da Daban Leda.

Makama ya rawaito, Abubakar Gamandi shugaban ƙungiyar masunta dake Tafkin Chadi na bada cikakken bayani yadda lamarin ya faru kamar yadda wasu da suka tsira da ransu suke bada labari.

“An kashe manoman mu bayan da suka je matartarar ISWAP su yi noma sun shirya da kungiyar ISWAP inda suka biya su kuɗi,” a cewar Gamandi

Gamandi ya cigaba da cewa  wani tsagin na kungiyar ta ISWAP da basu san da wancan yarjejeniya ne ba su ka kai musu hari kamar yadda wasu da suka tsira daga harin suka bayyana.

Ya ƙara da cewa sai manoman sun gama dawowa ne kawai za a tabbatar da yawan mutanen da suka mutu.

More from this stream

Recomended