
Wani jirgin bayar da horo na rundunar sojan saman Najeriya ya fado a Makurdi babban birnin jihar Benue.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya, Edward Gbkwet ya fitar ya ce jirgin ya fado ne lokacin da ake bada horo kamar yadda aka saba yi a ko yaushe a ranar Juma’a.
Gbkwet ya ce ba a samu asarar rayuka ba amma matuka biyu dake jirgin na can na samu kulawar likitoci a asibitin rundunar sojan saman dake Makurdi bayan da suka fice ta lema daga cikin jirgin.
Sanarwar ta ce babban hafsan sojan saman Najeriya , Hassan Abubakar ya kafa kwamitin bincike da zai gano musabbabin faruwar lamarin.