Matsalolin da suka yi wa Kannywood ‘tarnaki’ | BBC Hausa

.

Hakkin mallakar hoto
INSTAGRAM/@FALALU_A_DORAYI

A cikin ‘yan kwanakin nan, kungiyar shirya fina-finai ta Kannywood ta samu kanta cikin kalubale iri daban daban.

Sau da dama idan aka toshe nan, sai can ya balle, haka dai masana’antar ke ta gungurawa.

Manyan matsalolin da suka dabaibaye wannan kungiya sun hada da matsalolin siyasa da na shugabanci tsakanin ‘yan kungiyar da rashin hadin kai.

Amma babbar matsalar da ake gani ta yi kaurin suna a shekarun nan ita ce yadda wasu ‘yan fim din ke yin takun sama ko kuma zaman doya da manja tsakaninsu da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Masu sharhi dai na ganin idan irin wadannan matsalolin suka ci gaba, za su iya yin illa ga hanyoyin da dubban mutane ke amfana da su wajen samun abubuwan biyan bukata.

A nasa bangaren, Ishaq Sidi Ishaq wanda tsohon hannu ne a harkar fina-finan Hausa, ya bayyana wa BBC cewa daya daga cikin babbar matsalar ita ce ‘yan Kannywood sun jahilci ita kanta hukumar tace fina-finai wadda a yanzu Isma’il Na’abba Afakallah ya ke jagoranta.

Ya bayyana haka ne a cikin shirin ra’ayi riga na BBC inda ya ce hanya daya da za a fahimci wannan hukuma ita ce shirya taruka na wayar da kan jama’a kan dokokin hukumar.

Ya ce ”wasu da suke cikin masana’antar sun dauka aikin hukumar kawai shi ne ta tace fim”.

Sai dai a nasa bangaren Isma’il Afakallahu wanda shi ne shugaban hukumar ya bayyana cewa, ko a 2018 sai da hukumar ta shirya taron horaswa na musamman domin sanin ainahin mece ce hukumar tace fina-finai.

Sai dai duk a cikin shirin na ra’ayi riga, tauraruwa a Kannywood Rahama Sadau ta bayyana cewa ita bata taba jin an yi wani taron wayar da kai ba kan hukumar tace fina-finan.

Hakkin mallakar hoto
OTHERS

Ta bayyana cewa ba a taba gayyatarta irin wannan wayar da kan ba kuma bata taba jin an yi ba.

  • Ana takaddama tsakanin Baban Chinedu da hukumar fina-finai ta Kano kan marigayi Ibro

A wani bangaren kuma, wata daga cikin matsalar da ake ganin ta haifar wa Kannywood din rashin jituwa ita ce siyasa da wasu daga cikin ‘yan masana’antar suka tsunduma inda dayawa daga cikin ‘yan Kannywood din suka fito kararara suka nuna matsayarsu a siyasance musamman a zaben da aka gudanar na 2019.

Wasu suna ganin wadannan matsaloli na siyasa kuma sun haifi wasu matsaloli sabbi na daban wadanda ke ci gaba da ci wa Kannywood din tuwo a kwarya.

Ba abu bane a boye cewa wasu ‘yan fim din na bayan jam’iyyar adawa ta PDP wasu kuma na bayan jam’iyya mai mulki ta APC domin kuwa, an ga yadda wasu daga cikin ‘yan fim din suka rinka fitowa domin kwarzanta gwanayensu musamman a shafukan sada zumunta a lokacin yakin neman zabe.

Hakkin mallakar hoto
INSTAGRAM/@NAFEESAT_OFFICIAL

Shi kan shi Salisu Muhammad officer wanda shi ne mataimakin sakataren shugaban kungiyar MOPPAN na kasa ya shaida a cikin shirin ra’ayi riga cewa siyasa ta shiga cikin wannan masana’anta sai dai rokon Allah kawai.

Shi ma Ibrahim Sheme wanda mai sharhi ne kan fina-finan Hausa ya bayyana cewa siyasa na daya daga cikin abubuwan da ke rarraba kawunan ‘yan fim din.

Ya bayar da misali da harkar waka inda ya ce ”idan aka samu wani mutum ya yi waka ya soki wani mutum wanda ke mulki a Kano, wannan za ayi farautarsa duk inda ya ke a kamo shi.

”Amma idan wani wanda yake da ra’ayin gwamnatin Kano yayi waka ya zagi mutane, da wuya a kama shi.”

Sai dai Afakallahu ya musanta irin wadannan zarge-zarge da Ibrahim Sheme ya yi.

Sai dai a nata bangaren, Rahama Sadau ta bayar da shawara kan cewa bai kamata a ce an fito har a rediyo ba ana tattauna matsalar Kannywood, ya kamata a zauna ne zaman sulhu domin gaba dayansu ‘yan gida daya ne domin su tattauna matsalolinsu.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...