Matsalar tsaro: Gwamnoni ne abin zargi, ba Buhari ba—Orji Kalu

0

Tsohon gwamnan Jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ya wanke Shugaba Buhari game da matsalar tabarɓarewar tsaro a Najeriya, yana mai cewa sakacin gwamnoni ne ya tsunduma ƙasar halin da take ciki.

Mista Kalu ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Arise TV a ranar Alhamis.

Najeriya dai tana fama da mastalolin Boko Haram, da rikicin makiyaya da manoma da na ƴan satar mutane a arewa maso yamma, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here