Matawalle Ya Jagoranci Tawagar Hafsoshin Tsaro Ya Zuwa Jihar Filato

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya jagoranci tawagar manyan hafsoshin rundunar sojan Najeriya a wata ziyara da suka kai jihar Filato.

Ministan na tare da babban hafsan sojan Najeriya, Gabriel Musa, Taoreed Lagbaja shugaban rundunar sojan Najeriya, Emmanuel Ogalla shugaban sojan ruwan Najeriya da kuma Hassan Abubakar babban hafsan sojan saman Najeriya.

Betta Edu ministan jin kai da kawar da talauci na daga cikin tawagar da suka isa jihar ta Filato.

A jajiberin Kirisimeti ne aka kashe sama da mutane 115 a wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi da kuma Mangu a jihar Filato.

Matawalle ya ce batun matsalar tsaro ba abu ne da ya kamata a ce mutane sun cigaba da gani a cikin talabijin dinsu ko kuma karantawa a shafukan jarida inda ya yi alkawarin cewa za a samu sauyi kuma al’umma za su gani.

A yayin da yake magana da yan jarida ministan ya ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bawa jami’an tsaro umarni da su zakulo maharan a duk inda suke tare da hukunta su.

Ana ta bangaren ministar jin kan ta ce ma’aikatar ta za ta bayar da tallafi ga mutanen da abun ya shafa.

More from this stream

Recomended