Matatar man fetur ta Dangote ta shirya sayo ɗanyen man fetur daga kasar Amurka.
A cewar wani rahoton jaridar kasuwanci ta Bloomberg cinikayyar da aka ƙulla ta sayen man ya nuna yadda ɗanyen mai na kasar Amurka ke gogayya a kasuwar duniya.
Rukunin kamfanin Trafigura Group ya sayarwa da matatar ta Dangote ɗanyen man fetur nau’in West Texas Intermediate da za a kai matatar a ƙarshen watan Faburairu kamar yadda wasu majiyoyi suka fadawa jaridar.
Wannan ne dai karo na farko da babbar matatar man fetur ɗin take sayan ɗanyen mai wanda ba daga Najeriya aka haƙo shi ba.
Amma kuma ƴan kasuwar dake harkar ɗanyen mai sun gaza bai yana dalilin da yasa matatar mai dake cikin ƙasa mai cike da arzikin mai za ta riƙa sayo ɗanyen man fetur daga kasar Amurka inda suka ke ganin cewa hakan baya rasa nasaba da farashi.