Matatar Dangote Ta Sauke Farashin Man Fetur Zuwa N890

Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890, tare da fara aiwatar da sabon farashin tun daga jiya, Asabar, 1 ga watan Fabrairu, 2025.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, matatar ta bayyana cewa ragin ya biyo bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Dangote ya ce wannan matakin yana cikin manufarta ta tabbatar da gaskiya da adalci a kasuwanci, domin a duk lokacin da farashin duniya ya ragu, ita ma za ta rage domin amfanin al’umma.

Haka nan, matatar ta bayyana cewa tana da yakinin wannan ragi zai taimaka wajen saukaka farashin mai a faɗin Najeriya, wanda hakan zai rage tsadar kayayyaki, ayyuka, da kuma rayuwa gaba ɗaya.

A ƙarshe, ta yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da mai da su bayar da haɗin kai wajen aiwatar da sabon farashin, domin al’ummar Najeriya su amfana da rangwamen.

More from this stream

Recomended