Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa INEC ta ce an ƙona ofishin hukumar dake yankin Sankara a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue.
A wata sanarwa ranar Laraba, Sam Olumekun kwamishinan hukumar na sadarwa da kuma wayar da kan masu kaɗa riƙa ya ce Sam Egwu kwamishinan zaɓe na jihar ne ya bayyana haka.
Ya ce matasan yankin dake gudanar da zanga-zanga kan matsalar ƴan fashin daji a yankin su ne su farma ofishin hukumar da kuma wasu ofisoshin gwamnati da ƙarfe biyu na rana.
Sanarwar ta ƙara de cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba amma an samu asarar kayayyaki ofisoshi da kuma na aikin zaɓe.