Matasa a Kano, Jigawa da Sokoto za su ci gajiyar tallafin karatu na Tarayyar Turai

An zabi jihar Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da za su ci gajiyar sabon shirin samar da ilimi da karfafawa na Tarayyar Turai a wani shirin tallafi a Najeriya.

Shirin na da nufin kara yawan ’yan mata da maza da ke cin gajiyar damar koyo da fasaha masu inganci a jihohin Kano, Jigawa da Sokoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ya fitar kuma ya raba wa manema labarai a ranar Talata.

Shugaban tawagar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Michael Banda, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Doguwa game da shirin a ofishinsa a ranar Talata.

More from this stream

Recomended