
Hakkin mallakar hoto
AFP
Ebtekar – daya daga cikin mataimakan shugaban kasar Iran ta kamu da coronavirus
Mataimakiyar shugaban kasar Iran na daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar da suka kamu da cutar coronavirus a baya-bayan nan.
Rahotanni daga Iran na cewa coronavirus din mataimakiyar shugaban kasar ta yi tsanani amma ba a kai ta asibiti ba.
Gwamnatin Iran ta sanar da mutuwar mutum 26 ta dalilin coronavirus da ta kama mutum 245 a kasar.
Manyan jami’an gwamnatin kasar sun kamu da cutar, ciki har da mataimakiyar shugaban kasar da mataimakin Ministan Lafiya Iraj Harirchi.
‘Yan majalisar dokokin kasar guda biyu na daga cikin wadanda da suka kamu da cutar. Daya daga cikin ‘yan majalisar ya fito ne daga birnin Qom.
”Yaduwar cutar coronavirus a Iran na iya fin yadda ake zato,” in ji Michael Ryan na Hukumar Lafiya ta Duniya.
Ya ce duk da cewa kasar na da ”ingantaccen bangaren lafiya,” mutuwar kashi 10% na masu cutar a kasar na nufin gwajin da ake yi ba ya gano masu cutar idan ba ta yi tsanani ba.
Ma’aikatar Lafiyar Iran ta bukaci ‘yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye a kasar sai in yin hakan ya zama dole.
Makwabtan kasar sun rufe iyakokinsu da ita, yayin da aka samu bullar cutar a Hadaddiyar Daular Larabawa, da Kuwaita da Bahrain da Lebanon da Afghanistan da Pakistan, da Estonia, yawancinsu bayan dawowarsu daga Iran.