Masu sankarar mama na tsaka mai wuya

Maganin ciwon sankara


Wata babbar damuwar ita ce yadda magungunan cutar Sankara ke kara tsada a duniya

Cutar sankarar mama ko Cancer a turance, ciwo ne mai raunana jiki to amma hakan ba ya na nufin ba a iya magance shi ba.

Sankarar mama ta fi shafar mata, kuma babu ruwan ciwon da kankantar shekaru, ko yawan shekaru ko macen da ta haihu da wadda ba ta taba haihuwa ba.

Mata a nahiyar Afirka musamman a kasashe masu tasowa da masu karancin tattalin arziki na fuskantar matsalar shan magani da yin tiyata dan cirewa ko yanke mama baki daya.

A kasar Saliyo, matan sun dogara ne da dan tallafin da suke samu daga kungiyoyi na ciki da wajen kasar, sai dai ba abu ne mai sauki ba jumurin shan magani.

Wakilin BBC Umaru Fofana ya zanta da wasu daga cikin irin matan da ke cikin wani yanayi da babu yadda suka iya da cutar sai zubawa sarautar Allah ido da dogaro ga kungiyoyin da ke taimaka musu da magani kyauta.

Wata matashiya mai suna Khadija da ke aikin sa kai a wata cibiya mai suna Think Pink a turance da Umaru ya yi kicibis da ita a dakin da ake duba masu fama da lalurar a wani asibiti da ta ke aikin, ta shaida masa yadda ta samu kanta rana tsada da cutar sankarar, amma daga bisani ta warke.

A shekarar 2014 aka gano ta na dauke da ciwon, ta kuma samu gatan an kai ta kasar Ghana inda akai mata aiki tare da cire maman baki daya. A halin da ake ciki Khadija na burin zama malamar jiyya.

Sai dai lamarin ba haka ya ke ga wata matashiya mai suna Fatou, wadda marainiya ce kuma cutar ta bayyana tun ta na makarantar firamare har sakandare ta ke jin alamar wani abu a cikin maman ta, ba ta san ciwo ba ne har sai da ga baya lokacin da ta je asibiti.

An yi nasarar yanke tsiron, amma ya sake dawowa har sau biyu daga bisani an cire duka mamunan guda biyu to amma ciwon ya sake tsirowa. A yanzu Fatou ta na dauke da juna biyu da dole sai an kai ta kasar waje dan yi mata aiki a ceto rayuwar ta da ta jaririn da ke cikinta.

A yanzu dai cibiyar Think Pink ce ke wayar da kan mata a kasar Saliyo, da zarar sun ji wani sauyi da basu amince da shi ba su garzaya asibiti dan a duba su a kuma shawo matsalar tun kafin ta girma.

Think Pink na taimakawa matan da suka samu kansu da wannan lalura da magunga, ana kuma fatan za a samu tallafin yi wa Fatou aiki dan ceton lafiyarta.

Babbar matsalar da kasar Saliyo ke fama da ita shi ne karancin likitoci, inda al’umar kasar miliyan bakwai suka dogara ga likitocin da ba su kai 200. Cikin wadannan likitoci dai guda daya ne likitan Zuciya, da likitan kashi daya, sannan babu likita ko daya a fannin jijiyoyi da ciwon daji.

Wannan na daga cikin dalilan da ke janyo koma baya ta fannin kiwon lafiya a kasar da ta yi fama da yaki da yaduwar cututtuka masu saurin kisa, misali cutar Ebola.

More News

Jihar Ogun za ta riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya amince a riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi girma ƙarancin albashi a jihar. Sakataren gwamnatin jihar, Tokunbo Tlabi ya...

Jihar Ogun za ta riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya amince a riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi girma ƙarancin albashi a jihar. Sakataren gwamnatin jihar, Tokunbo Tlabi ya...

Kamfanin Maltina ya karrama malamin da ya zama gwarzon shekara

Esomnofu Ifechukwu daga makarantar Crown Grace, Mararaba, jihar Nasarawa, ya zama zakaran gasar Maltina Teacher of the Year karo na 10 a babban taron...

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...