Masu ‘ra’ayin rikau’ na shirin lashe zaben majalisar dokokin Iran | BBC Hausa

Ayatollah Ali Khamenei (08/02/20)
Hakkin mallakar hoto
EPA
Image caption

The parliament is subservient to Iran’s supreme leader

‘Yan kasar Iran suna kada kuru’unsu a zaben’yan majalisar dokokin da aka yi amannar cewa masu tsattsauran ra’ayin da ke goyon bayan shugaban addinin kasar ne za su yi nasara.

Shi ne karon farko da ake gudanar da zabe tun bayan da Amurka ta sake kakaba wa kasar sabbin takunkumai saboda shirinta na samar da makamashi da ke amfani da nukiliya, lamarin da ya gigita tattalin arzikin kasar.
An hana dubban masu tsaka-tsakin ra’ayin addini fafatawa a zaben saboda rashin cika tsauraran ka’idojin da aka shimfida.
Masu sanya ido sun ce hukumomin kasar na fatan mutane za su fito sosai su kada kuri’unsu saboda sun nuna wa duniya cewa ‘yan kasar suna goyon bayan gwamnati.
Masu sukar shugabannin Iran sun yi kira ga ‘yan kasar su kaurace wa zaben domin bijirewa abin da suka kira take hakkin dan adam da rashin bari a fadi albarkacin baki a kasar.

Related Articles