Wasu masu kutse da suke ikirarin sun fito daga Iran sun kwace iko da shafin Intanet mallakin gwamnatin Amurka inda a shafin suka wallafa wani sakon nuna goyon baya ga Iran.
Mutanen da suka ziyarci shafin a ranar Asabar sun ga wani hoton Shugaban Amurka, Donald Trump da aka wallafa jini na fita ta bakinsa.
Sannan kuma a gefen hoton an rubuta wani sako da ke cewa masu kutsen sun yi haka ne a wani mataki na mayar da martani kan kisan kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani.
Kawo yanzu, babu rahoton da ya tabbatar da cewa gwamnatin Iran ce ta dauki nauyin lamarin.
Sakon wanda a yanzu aka goge na cewa “shahada ita ce ladan da Soleimani ya samu tsawon shekarun da ya shafe yana hidima.”
“Duk da ya rasu, ayyukansa da kuma kokarin da ya yi ba za su gushe ba sannan kuma mummunan mataki na jiran wadanda suka kashe shi da sauran wadanda suka yi shahada.”
Kutsen da aka yi ta shafin intanet din na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan Iran ta sha alwashin mayar da martani kan Amurka bisa kisan Soleimani duk da gargadin da masu sharhi ke yi game da hare-hare ta kafar intanet da Iran ke kaiwa kan Amurka.
Wani mai magana da yawun hukumar tsaro ta intanet ta ce ta na “sa ido” kan lamarin.
“Mu na sane da kutsen da aka yi wa shafin (Federal Depository Library Program) na intanet wanda aka wallafa wani sakon kin jinin Amurka,” kamar yadda hukumar tsaron ta fada cikin wata sanarwa.
“Tuni an rufe shafin kuma ba a iya shiga.”
Sanarwar ta kuma bada shawarar duk hukumomi su kara sa ido kan shafukansu na intanet domin kauce wa masu kutse su kuma tanadi matakan kare kansu.
Jake Moore, wani kwararre ne kan harkar tsaron intanet a kamfanin Eset, ya shaida wa BBC cewa yaki ta kafar intanet wata barazana ce ga al’umma.
“Wannan barazanar a wasu lokutan ta fi fito-na-fito ma’ana kasashe da masu kutse a intanet za su ci gaba da samun dama tun da komai zai iya faruwa,” a cewarsa.
“Rashin sanin irin barazanar da ke tafe na iya yin tasiri a fannoni da dama har da hannun jari.
Soleimani mai shekara 62 ya jagoranci dakarun Iran a yankin gabas ta tsakiya inda kuma Amurka take kallon sa a matsayin ‘dan ta’adda’.
Sabon shugaban dakarun Kurdawan Iran da Soleimani ya jagoranta ya yi ikirarin cewa kasar za ta fara korar Amurka da ga yankin na gabas ta tsakiya.
“Mun dauki alkawarin dorawa da ga inda Soleimani ya tsaya kuma fansa a wajenmu ita ce ganin Amurka ta fice daga yankin,” kamar yadda gidan rediyon kasar ya rawaito Esmaiil Qaani ya na fada.
Amurka dai ta shawarci al’ummarta da su fice daga Iraki kuma ta aike da karin dakarunta 3,000 zuwa gabas ta tsakiya.