Masu juyin mulkin Nijar sun ayyana sabon firaminista

Kusan makwanni biyu bayan da sojoji suka karbe mulki a Nijar, masu juyin mulkin sun nada tsohon ministan tattalin arzikin kasar Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin sabon Firaministan kasar.

Mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojan ne ya bayyana hakan a gidan talabijin da yammacin jiya Litinin.

Lamine Zeine ya taba rike mukamin ministan tattalin arziki da kudi na shekaru da dama a majalisar ministocin shugaban kasar Mamadou Tandja da aka hambarar a shekara ta 2010, kuma a baya-bayan nan ya yi aiki a matsayin masani kan tattalin arziki a bankin raya Afirka a kasar Chadi, a cewar wani rahoto da kafar yada labaran Nijar ta fitar. .

A karshen watan Yuli ne sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum tare da dakatar da kundin tsarin mulki a kasar mai mutane miliyan 26.

More from this stream

Recomended