Najeriya ta tabbatar cewa kawo yanzu mutane 30 ne aka tabbatar suna dauke da Coronavirus amma tuni aka sallami mutane biyu bayan da suka warke daga cutar.
A cewar hukumar dake lura da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC mutane biyu da aka samu dauke da cutar suna jihar Lagos biyu daga cikinsu sun dawo ne daga kasar waje ya yin da daya daga ciki kuma ya yi cudanya da wani da yake dauke da cutar.
Hukumar ta NCDC ta tabbatar da haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.