—BBC Hausa
Hakkin mallakar hoto
Muhammadu Buhari Twitter
Shugaba Muhammadu Buhari na halartar Bikin Kamun Kifi na Argungu karon tun bayan sama da shekara goma saboda matsalar tsaro
Fadar shugaban Najeriya ta ce an hana mutumin mai tsananin shaukin nuna goyon bayansa ga shugaba Muhammadu Buhari isa jikinsa ne saboda haka matakai suka tanada a duk fadin kasashen duniya.
Babban mashawarcin shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya ce matashin wanda ya so isa wurin Muhammadu Buhari ya je ne don kawai ya gaishe shi kuma ya nuna masa goyo baya.
Sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, don kuwa ya gamu da cikas, daga jami’an tsaro.
Femi Adesina ya bayyana mamakin abin da ya ce yadda a yanzu wasu ‘yan adawa ke nuna lamarin tamkar wani yunkurin kai wa Shugaba Muhammadu Buhari hari.
- Muhammadu Sanusi II: ‘Kaduna mun tsinci dami a kala’
- Yadda aka yi wa Buhari ihu a yayin ziyararsa a Maiduguri
Tun da farko wani bidiyo da ke nuna wani matashi cikin bakaken tufafi cikin sauri ya yi yunkuri ya nufi shugaban kasar tare da wasu manyan jami’an gwamnati lokacin da suka jeru a gaban wani tsibin buhunnan shinkafa ana dauke su hoto kafin jami’an tsaro su rike shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya je jihar Kebbi ne ranar Alhamis don bude Bikin Kamun Kifi da Nunin Al’adu na Argungu na bana.
An shafe tsawon sama da shekara goma ba tare da yin bikin na Argungu ba, saboda matsalar tsaro da sauran kalubalan da suka sha kan masu shirya bikin al’adar.
Hakkin mallakar hoto
Femi Adesina
Wasu bayanai sun ce mutumin ya sheka kan Shugaba Buhari ne a wurin wannan taro da ya yi cikar kwari yana cewa ‘A bari mu gaisa da Baba Buhari’.
Sai dai Femi Adesina ya ce jami’an tsaro ba za su bar hakan ta faru ba a ko’ina cikin fadin duniya.
Don haka a cewarsa, suka hana mutumin isa ga shugaban kasa, inda shi kuma ya shiga magiya don nema a bar shi ya gai da Buhari.
YYa ce mutane masu neman jafa’i a kullum sukan juya al’amura su ba su wata muguwar fahimta.
Sai dai in ji shi a wannan karo Allah ya wargaza aniyar masu bakar aniya, yayin da Najeriya ta ci gaba da rayuwarta.