Masinja ya daɓa wa manajan gidan karuwai wuƙa

A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke Ogudu a jihar Legas ta bayar da belin wani ma’aikaci da ya daba wa manajan gidan karuwai wuka a kan kudi N200,000.

An tuhumi masinjan dan shekara 24, Huzairu Shehu, wanda ke zaune a unguwar Gengere da ke Mile 12 Ketu, jihar Legas da laifin haddasa mummunar barna.

Sai dai ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Alkalin kotun, Mrs M.O. Tanimola, ya kuma umurci wanda ake kara da cewa ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa.

Ta ɗage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 18 ga watan Oktoba. Tun da farko, mai gabatar da kara, Insp Donjiur Perezi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Satumba a Gengere.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...