Manjo Al-Mustapha Yace Wasu Manya ke Haddasa Rikici A Nigeria

[ad_1]

Yayinda ake kasafin kudin da aka ce tsohon shugaba marigayi Sani Abacha ne ya sace, tsohon dogarinsa Manjo Hamza Al-Mustapha yace har yanzu ya na mamaki game da zargin kuma akwai ayar tambayoyi.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana wanan damuwar ne a lokacin wani taro da gamayyar shugabannin kungiyoyn Kiristoci suka kira a jihar Kaduna.

Ya ce kudi da ake zargin tsohon shugaba Abacha ya sace, yaushe aka ajiye su a banki? Kafin ya zama shugaban kasa ne ko bayan ya zama shugaban kasa? Ya ce wa ya dauko kudin? Me ya sa suke gaggawan rabawa? Kudin farko da aka raba mutane nawa suka dauki kudin suka gudu?

Manjo Al-Mustapha y ace ana zargin Abacha da satar dala miliyan 300 amma yau akwai shugaban karamar hukuma da ya yi gaba da fiye da tiriliyoyin Naira ko biliyoyin dala. Akwai kudin da aka sace daga Nigeria a Amurka. Ire iren wadanda suka sace kudin kasar su ne suke haddasa fitina saboda su zauna lafiya yayinda suke jefa mutane cikin zaman zullumi.

Dangane da tsananin tsamin tsaro a wasu sassan kasar Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce akwai sa hannun wasu. Yace yawan amfani da miyagun ‘kwayoyi da ta addabi arewa da gangan ake turo ta, kuma da hannu wasu manya a ciki” Yace an rena arewa ne, an mayar da mutanenta tamkar dabbobi. Ya kara da cewa makaman da aka shigo dasu domin a ci zabe an taba tambayar inda suke? Ko kuma ake inda ake ajiyesu?

Game da kiran da aka yi masa a wurin taron cewa ya fito ya shiga takarar shugaban kasa , yace abun da suka fada ra’ayinsu ne kawai.

Bisa dalilin da ya sa gamayyar kungiyoyin Kiristoci ta kira ya tsaya takara, Pastor Aminci Habu wanda ya jagoranci kungiyoyin ya ce suna neman su fita daga wahala da matsalolin da suke ciki. Saboda haka suka gayyato Manjo Al Mustapha domin su tattauna dashi kana su tabbatar masa suna son ya nemi shugabancin kasar.

A saurari rahoton Isa Lawal Ikara domin karin bayani

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...