Man City za ta san makomarta a Champions League ran Litinin

Manchester City's Etihad Stadium

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City ta buga gasar Zakarun Turai ta Uefa sau 10 ba ta taba lashe kofin ba

Ranar Litinin Manchester City za ta san makomarta a gasar Zakarun Turai, bayan daukaka kara da ta shigar kan dakatar da ita kaka biyu da UEFA ta yi.

City ta daukaka kara zuwa kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya, (Cas,) bayan da hukumar kwallon kafa ta Turai ta hukunta kungiyar ta Etihad.

Uefa ta ce ta samu City da karya dokokinta da dama ciki har da ta kashe kudade ba bisa ka’ida ba tsakanin 2012 zuwa 16.

Haka kuma an ci tarar Manchester City fam miliyan 25.

Tun da hukumar kwallon kafa ta Turai ta yanke wa City hukuncin, kungiyar ta ce za ta daukaka kara ga kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya.

A cikin watan Juni aka saurari daukaka karar da City ta shigar, inda Alkalan suka ji bahasin City da na Uefa ta fasahar bidiyo, amma a asirce.

Idan har City ba ta yi nasara ba, to ba za ta shiga gasar Zakarun Turai ta badi ba, sannan ba za ta fafata a Uefa Super Cup a gaba ba, koda ta lashe Champions League na bana.

City za ta karbi bakuncin Real Madrid a Etihad a wasa na biyu na kungiyoyi 16 da ke gasar Champions League ranar 7 ko kuma 8 ga watan Agusta.

Kungiyar ta Etihad ta yi nasarar doke Real Madrid da ci 2-1 a wasan farko da suka yi a Madrid, idan ta yi nasarar kai wa zagayen gaba za ta kara da Juventus ko kuma Lyon a wasan Quarter finals a Lisbon.

More News

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...

An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naɗa, Muhammad Sanusi a matsayin...