Man City ta kai zagaye na biyar a FA Cup

Manchester City ta doke Burnley

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City ta samu nasarar zuwa zagaye na biyar a gasar FA bayan ta lallasa Burnley ci 5-0.

Gabriel Jesus da Bernardo Silva da Kevin de Bruyne da Sergio Aguero ne suka ci wa City kwallayen a ragar Burnley.

Pep Guardiola wanda ya lashe wa City kofin Premier da Carabao a bara, yana harin lashe kofi hudu a kakar bana.

Manchester City za ta hadu da Chelsea a wasan karshe na kofin Carabao, sannan za ta hadu da Schalke a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

City da ke matsayi na biyu a teburin Premier, tazarar maki hudu ne ya raba ta da Liverpool da ke jan ragamar teburin, kuma ga shi yanzu ta kai zagaye na gaba a gasar FA.

City ta ci kwallaye 30 a wasanni bakwai da ta buga a 2019.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...