Makusanta Buhari da suka mutu tun da ya hau mulki

Buhari

Bayanan hoto,
Abba Kyari da Isma’ila Funtua sun kwashe shekara da shekaru suna mu’amala da Shugaba Muhammadu Buhari

Rasuwar da Isma’ila Isa Funtua ya yi ranar Litinin da yamma ta girgiza Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Da alama ya girgiza ne ganin cewa Isma’ila Isa Funtua, wanda na hannun damansa ne, ya mutu ne watanni kadan bayan rasuwar Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Da yake bayyana ta’aziyyarsa kan rasuwar Alhaji Ismai’la Isa Funtua, Shugaba Buhari ya ce mutuwarsa ta bar babban giÉ“i.

Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai ba shi shawara kan kafafen yaÉ—a labarai ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin “mutum na kowa da ake matuÆ™ar girmamawa.”

Malam Isma’ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin suna da tasiri a gwamnatin Buhari.

Shugaba Buhari ya ce rasuwar ministan na Jamhuriya ta biyu ta haifar da babban giɓi ne kasancewar ya taimaka masa musamman a tafiyarsa ta siyasa.

Rasuwar Ibrahim Dauda da Mutari Dauda

Wasu daga cikin makusantan Shugaba Buhari da suka mutu a wannan shekara sun hada da Irahim Dauda, dan yayansa shugaban kasar.

Ya rasu ne ranar 30 ga watan Mayu kwana kadan bayan rasuwar wani dan yayan nasa Mutari Dauda, wanda ya mutu ranar 8 ga Mayun 2020, a cewar sanarwar da kakakin shugaban kasar Malam Gatrba Shehu ya fitar.

Haka kuma shugaban kasar ya rasa ‘yar uwarsa Hajiya Halima Dauda, mahaifiyar Sabiu Tunde, daya daga cikin masu taimaka masa.

A sakon ta’aziyyarsa, Buhari ya ce rasuwarsu ta raba iyalansu da ma al’umar Daura, wato mahaifarsa da wasu daga cikin mutane na gari.

Ya ce: “Na yi matukar kaduwa da jin mutuwar wani dan uwan nawa, mutumin da yake da matukar kirki da gaskiya a mu’amalarsa.”

Abba Kyari: Na yi rashin babban amini – Buhari

Kazalika a watan na Mayu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Abba Kyari ya rasu, kuma shugaban kasar ya bayyana shi a matsayin “babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa”.

Cikin wata sanarwa da shugaba Buhari ya fitar mai taken ‘Zuwa ga Abokina Abba Kyari’ ya ce amininsa ne tun shekara 42 da suka gabata kafin daga baya ya zama shugaban ma’aikata a fadarsa.

Malam Abba Kyari ya rasu yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

Shugaba Buhari ya ce Abba Kyari wanda ya fara haduwa da shi tun yana saurayinsa dan shekara 20, “bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen sadaukar da kai ga ci gaban kowannenmu.”

“Abba Kyari, mutumin kwarai ne da ya fi mu,” in ji Buhari.

Ya kuma ce kasancewar Abba Kyari shugaban ma’aikata a fadarsa a 2015, “ya yi iya kokarinsa ba tare da nuna kansa ba ko neman mallakar abin duniya wajen aiwatar da burina.”

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...