Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Barcelona ta yi wa kaftin ɗinta ɗan ƙasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 32 tayin sabuwar yarjejeniya domin ya ci gaba da murza leda a kulob din har 2023. (Mundo Deportivo via Metro)
Dan wasan gaba na Sifaniya Pedro, mai shekara 32, ya amince ya koma Romaamma zai yanke shawarar ko zai tsawaita zamansa na ɗan wani lokaci a Chelsea har zuwa ƙarshen kaka. (Guardian)
Pedro ba ya son kammala kaka tare da Chelsea domin ba ya son a samu cikas kan komawarsa Roma. (The Athletic – subscription only)
Dan wasan tsakiya dan kasar Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana son sama da fan £100,000 duk mako domin samun wakili bayan ya yi watsi da yarjejeniyar da Bournemouth ta taya masa kan ya ci gaba da taka leda har zuwa ƙarshen kaka. (The Times – subscription only)
- Za a kammala Champions da Europa League cikin watan Agusta
- Manchester United tana son ɗauko Willian, Everton tana zawarcin Allan
Leicester City ba ta son sayar da ɗan wasan Ingilila mai shekara 23 Ben Chilwell idan an bude kasuwar musayar ƴan wasa ko da kuwa an taya ɗan wasan kan kan fam miliyan £50. (Sky Sports)
Bayern Munich na tunanin sayar da dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 27. (Telegraph – subscription only)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya buƙaci shugabannin kulub din mara masa baya domin ya yi zubin sabbin ƴan wasa idan an bude kasuwar musayar ƴan wasa – bayan Chelsea ta amince ta kashe fan miliyan 54 domin karɓo ɗan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 24, daga RB Leipzig. (Mirror)
Ɗan wasan baya naMonaco Benjamin Henrichs, mai shekara 23, wanda Bayern Munich ke buƙata, akwai yiyuwar RB Leipzigza ta karɓe dan wasan (Bild Sport – in German)
Kaftin ɗin Orlando City ɗan ƙasar Portugal Nani, mai shekara 33, ya ce tsohon ɗan wasan Manchester United kuma abokin wasansa a Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya shaida masa cewa yana son ya taka leda a gasar Major League Soccer ta Amurka kafin ya yi ritaya. (ESPN)
KocinHuddersfield Danny Cowley ya yi imanin cewa kulub ɗin yana kan hanya mai kyau bayan yunƙurin tsawaita kwantaragin ƴan wasan da kulub ɗin ya karbo aro da suka haɗ da gola Jonas Lossl, mai shekara 31, da kuma ɗan wasan Ingila Trevoh Chalobah, mai shekara20. (Yorkshire Post)
GolanEvertonDan Rose, mai shekara 16, ya koma buga gasar Bundesliga a kulub ɗin Schalke. (Liverpool Echo)