Makomar Havertz, Willian, Rodriguez, Hojbjerg da Aarons

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelseata kara samun kwarin guiwar dauko dan wasan tsakiya na Jamus Kai Havertz daga Bayer Leverkusen bayan shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce ba zai iya sayen dan wasan ba mai shekara. (Sun on Sunday)

Inter Milan ta fa tattaunawa da Chelsea kan dan wasan baya Emerson Palmieri, mai shekara 25 daga Stamford Bridge. (Observer)

Chelsea ta bude tattaunawa da dan wasan Brazil Willian, wanda Arsenal da Tottenham, ke zawarcinsa bayan dan wasan na gaba mai shekara 31 ya yi watsi da tayin wani kulub din China. (Goal)

Real Madrid na son sayar da dan wasan tsakiya na Colombia James Rodriguez, wanda ya rage masa shekara daya kwangilarsa ta kawo karshe don gudun kada ya tafi kyauta a badi yayin da Arsenal, Everton, Manchester United da Wolves ake tunanin suna da sha’awa kan dan wasan mai shekara 28. (Marca)

  • Sane ya rattaba kwantiragi da Bayern Munich
  • Aubameyang ya ba Arsenal zaɓi, West Brom na son Mikel

Leicester City na son sake gwada sa’arta kan dan wasan baya na Denmark Jannik Vestergaard daga Southampton, bayan ta kasa sayen dan wasan a watan Janairu. (Goal)

Kocin Everton Carlo Ancelotti ya ce dan wasan Southampton Pierre-Emile Hojbjerg dan wasa ne mai kyau amma ya ki bayyana ko yana son dauko dan wasan na Denmark mai shekara 24.(Liverpool Echo)

Ancelotti ya ce babu yadda zai bari ya saki dan wasan baya na Everton Lucas Digne bayan dan wasan na Faransa ana alakanta shi da Chelsea da kuma Manchester City. (Sunday Telegraph)

Hojbjerg ma na cikin wanda Tottenham, ke hari baya ga dan wasan Ingila mai shekara 20 Max Aarons da take son karbo wa daga Norwich City. (Athletic, via Sunday Express)

West Ham ta shiga sahun su Everton, Manchester United da Southampton da ke sha’war dan wasan Real Valladolid da Ghana Mohammed Salisu, mai shekara 21. (Mail on Sunday)

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...