
Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta janye hanin da tayi na hana sayar da man fetur a garuruwan da suke da tazarar kilimita 20 daga kan iyakar Najeriya.
Majalisar ta zartar da matakin ne a ranar Talata biyo bayan kudirin da dan majalisa daga jihar Ogun, Adeboyega Isiaka ya gabatar.
Yan majalisar sun yi kira da hukumar kwastam ta Najeriya da kuma sauran hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su kyale gidajen mai da suke a garuruwan kan iyaka kuma suke da cikakkiyar rijista a rika kai musu.
A shekarar 2019 gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ta hana kai mai a duk wani gidan mai dake da tazarar kilimita 20 daga boda.
Gwamnatin ta bayar da umarnin ne a lokacin domin dakile fasa kwaurin man fetur da ake zuwa kasashe makota irin su Nijar, Kamaru, Benin Chad da kuma Togo.