Majalisar dattijai ta Najeriya ta yi kira ga sojojin Najeriya cewa su rika kai hari kan ‘yan bindiga maimakon su jira sai an kai musu hari su nemi fansa.
Ta kuma nemi gwamnatin tarayya ta samar da jiragen yaki domin fatattakar ‘yan ta’adda daga duka maboyarsu.
Wannan na cikin wasu abubuwa da aka cimma matsaya a kansu bayan dogon lokmacin da aka share ana muhawara kan tabarbarewar da tsaro ya yi a kasar.
‘Yan bindiga sun fadada ayyukansu a yankin jihohin arewa maso yammacin da suka hadar da Kaduna da Sokoto da Katsina da Kebbi da Zamfara da kuma Neja da ke yankin arewa maso tsakiya, inda suke ci gaba da kashe mutane da yawa da kuma tarwatsa kauyuka masu yawa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 1,192 kuma sun sace 3,348 a bara.
A makon jiya, sai da suka kashe 18 ciki har da wasu sojoji, tukunna aka jikkata mutum 40 yayin da ‘yan ta’addan suka mamaye kauyen Galadima Kogo a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.