Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu da ya mika mata ta neman korar dakatattun kwamshinonin zaɓen jihohin Adamawa, Sokoto da kuma Abia.
An amince da bukatar shugaban ƙasar ne bayan da Opeyemi Bamidele shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar kudiri kan batun a ranar Laraba.
Kwamishinonin su ne Ike Uzochukwu, (Abia), Hudu Yunusa-Ari, (Adamawa), da kuma Nura Ali (Sokoto).
Tinubu ya nemi amincewar majalisar ne na kawo ƙarshen aikin kwamishinonin ne kan aikata ba dai-dai.
Da yake gabatar da kudirin, Bamidele ya ce buƙatar shugaban ƙasar ta yi dai-dai da sashe na 157(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, Abba Moro shugaban marasa rinjaye ya ce korar ta su za ta zama izina ga waɗanda suke riƙe da mukamin gwamnati.