Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi gargaɗin cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsalar yunwa a wannan shekara, sakamakon raguwar tallafin agaji da ake samu a faɗin duniya.
Hukumar ta bayyana cewa kusan yara miliyan uku na cikin barazanar rashin samun abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara tsananta a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, inda rikice-rikice suka yi kamari.
Kodinetan hukumar ba da agaji na MDD a Najeriya ya ce a halin yanzu ba za a iya dogaro da irin agajin da aka saba bayarwa a baya ba, saboda ƙarancin kuɗaɗe.
MDD ta ƙara da cewa za ta mai da hankali ne kan ayyukan ceton rai kawai, inda za ta ware kusan dala 500,000 domin tallafa wa mutane miliyan biyu da rabi a fadin ƙasar.
Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Yi Gargaɗin Yunwa Ga Fiye Da Ƴan Najeriya Miliyan 30 A Bana

