Majalisa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

Majalisar dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Bayan haka kuma an tabbatar da nadin Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawar.

Tabbatarwar ta biyo bayan bayyanar Olukoyede da Hammajoda tare da rakiyar wasu ma’aikatan hukumar a zauren majalisar.

Wannan dai ya nuna gagarumin sauyi a shugabancin hukumar ta EFCC, yayin da Olukoyede ke rike da mukaminsa kusan watanni hudu bayan dakatar da tsohon shugaban, Mista Abdulrasheed Bawa da shugaba Tinubu ya yi.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...