Mafiya Yawan Estet-Estet Na Abuja Da Kuɗin Haram Aka Gina Su—EFCC

Hukumar yaki da cin hanci a Najeriya EFCC ta ce a yanzu hankalinta zai koma kan waɗanda ke fakewa da gina estet wajen cin kudaden haram.

Yayin da yake jawabi a wajen taron haras da ‘yan jarida a birnin Benin na jihar Edo, lauyan hukumar Chris Mishela ya ce da yawa daga cikin estet-estet da ake ginawa a Abuja da Legas da sauran yankunan ƙasar, ana gina su ne da kuɗaɗen haram.

Ya kuma ƙara da cewa, ”akwai rukunin gidaje masu yawa a Abuja, waɗanda muka yi amanna cewa an samu kuɗin gina su ta haramtattun hanyoyi”.

”Kuɗaɗen haram da yawa da aka samu ta ɓangaren gwamnati ko wasu miyagun laifukan da suka shafi kuɗi na duniya, ana amfani da su wajen kasuwancin rukunin gidaje”, in shi.

”EFCC na aiki domin bincike da kuma lura da wannan ɓangare, kuma sabuwar dokar halasta kuɗin haram ta bai wa gwamnati damar lura da bincike kan rukunin gidaje, kuma EFCC na ƙarƙashin gwamnati don haka muna aiki da dokar”.

“Ba iya binciken kawai muke yi ba, mun ma gano cewa wasu daga cikinsu an gina su ne da kuɗin haram.”

More from this stream

Recomended