Mai Shari’a Ayo Salami Ya Karyata Labarin Da Lauyoyin Magu Suka Yada Cewa Ya Yi Nadamar Karbar Aikin Da Yayi

Mai Shari’a Ayo Salami wanda ke shugabancin wannan kwamitin yayi tir da Allah wadai da, abin da ya kira labarin kanzon kurege da aka wallafa a cikin jaridu, wanda lauyoyin Ibrahim Magu ne suke cewa wai yayi juyayi da nadama a kan karban wannan shugabancin da aka bashi na kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

Ayo Salami ya nuna mamakinsa kan yadda aka ari bakinsa aka ci masa albasa. Malam Nasiru Zahradin ƙwararre a kan fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ya ce, “Tun ba yau ba ake irin wannan buge-buge a jaridu, musamman irin jaridun nan na zamani, su suke bubbuga waɗannan labarai, mutane masu goyon bayansa da lauyoyi ‘yan’uwansa suke ta sawa a kafar yaɗa bayanai domin su ga wannan kwamiti da aka kafa sun wargaza shi, sun ce abunda yake ba daidai ne ba”

Ya ƙara da cewa ya kamata hukuma ta tanadi hukunci ga masu irin wannan cin zarafi ga al’umma. A gurfanar da su gaban shari’a. Ya ce su kan su, kafofin yaɗa labarai da aka ce sun yi ta ƴaɗa labaran, wanda na kanzon kurege ne, su ma a hukunta su.

Abdulkarim Ibrahim wani ƙwararre a harkar intanet da yadda ake amfani da ita wajen yaƙi da cin hanci, ya jinjina wa Ayo Salami. Ya ce suna so ne a janye labarin da kowa ya riga ya sani, bai dace ba a ce komai ya faru sai a kai shi ga jarida, al’umma basa sanin me ake ciki sai dai a yi ta surutai a jarida a haka har abun ya wuce.

A wancan lokacin, lauyoyin na ganin suna burge shi don haka ma suka cigaba da irin wannan aikin. Amma Ayo Salami ya fahimci manufarsu, kuma ya ƙaryata cewa bai faɗi magan nan ba.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...