
Sojoji 2 da wasu mutane 15 aka bada rahoton an kashe a wani hari da wasu yan bindiga suka kai kan wasu ƙauyuka uku dake karamar hukumar Apa ta jihar Benue.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai harin ne a tare lokaci guda da misalin karfe 06:00 na yammacin ranar Talata kan ƙauyukan Opaha, Odogbo da kuma Edikwu dake karamar hukumar ta Apa.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Kole ya ce gawarwaki 17 aka gano a cikin daji ciki har da sojoji biyu na rundunar Operation Whirl Stroke lokacin da jami’an tsaro suke bincike a yankin da asubahin ranar Laraba.
Har ila ya bayyana cewa ɗaya daga cikin gawar sojojin ta kwamandan rukunin sojojin ne da suka yi kokarin dakile farmakin da maharan suka kawo.