Magoya bayan jam’iyyar PDP 616 sun koma APC a Gombe

Magoya bayan jam’iyar PDP 616 ne suka sauya sheka daga jam’iyar ya zuwa jam’iyar APC a karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe.

Jigo a jam’iyar ta PDP a Dukku, Alhaji Kwairanga Dukku shi ne ya jagoranci mutane 616 masu dauke da katin jam’iyar PDP da suka hada da mata da matasa wadanda suka fito daga mazabu 10 na karamar hukumar ya zuwa sakatariyar APC a karshen mako.

Ya ce sun ɗauki matakin sauya shekar ne saboda shugaban ci nagari da gwamna Inuwa Wada ya ke yi.

Ya ya bawa gwamnan kan tsare-tsaren da yake na inganta rayuwar al’umma.

More from this stream

Recomended