Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam’iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam’iyar APC da dama a jihar Kano.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi masu sauya sheƙar ya zuwa jam’iyar ta APC da suka fito daga ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono a madadin gwamnan jihar a gidan gwamnatin jihar Kano.

Wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar ta bakin, Ibrahim Garba Shu’aibu ta ce Gwarzo ya jaddada buƙatar fifita haɗin kai a jam’iyar inda ya tabbatar da za a kula da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Gwarzo ya ce gwamnatinsu ta mayar da hankali wajen aiwatar da tsare-tsare da za su amfani al’umma inda ya yi kira ga mutanen jihar su cigaba da basu goyon baya.

Da yake jawabi tun da farko jagoran masu sauya sheƙar, Alhaji Haruna Babangida Abbas (Kosasshe) ya ce ingancin shugabancin gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma salon gwamnatinsa na daga cikin dalilinsu na sauya sheƙar ta su.

More from this stream

Recomended