Mafi Yawan Masu Corona Basa Yarda Suna Da Cutar – Ministan Lafiya – AREWA News

Ministan kiwon Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa mafi yawan masu cutar Coronavirus babu wata alama a jikin su mai nuna su na dauke da ciwon.

“Kashi 80 bisa 100 na masu dauke da cutar Coronavirus a kasar nan, babu alamar da ke nuna cutar a jikin su.

“Dalili da yasa yake da wahalar gaske mu gamsar da su cewa akwai cutar a jikin su.

“Ko ka yi kokarin nuna musu ba za su amince da kai ba.Saboda su na jin garau a jikin su, amma kuma a talbijin su na ganin yadda ake nuno masu cutar ranga-ranga. Kuma su na ganin irin yadda suke mutu kwakwai rai kwakawai a Cibiyoyin Kula da Masu Cutar.

“Wasu kuma da sun ji su na da cutar, ba su jira a killace su sai kawai su tsere ko su boye, a neme su a rasa.

Da yawa su na guje wa killacewa.

Rahotanni da dama daga jihohi sun tabbatar da wasu kuma sun tsere daga inda ake killace da su.” Inji Ehanire.

Masu dauke da Cutar da dama sun tsere a Kano, Lagos, Gombe da sauran jihohi da yawa.

Wani likita Mai suna John Oghenehero, ya ce mutane na gudun killacewa ne saboda gani suke yi kamar an yi wa rayuwar su wani bakin tambari.

More News

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...

An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naɗa, Muhammad Sanusi a matsayin...