Mabiya shi’a sun nemi Najeriya ta yanke alaka da kasar Isra’ila

Kungitar Yan Uwa Musulmi ta Najeriya da aka fi sani da shi’a tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta yanke dukkanin wata alaka da hulɗa da kasar Isra’ila saboda hare-haren da suke kai wa a yankin Gaza.

Abdullahi Danladi mamba a kungiyar shi ne ya bayyana haka a wurin wani taron manema labarai da suka kira a Abuja inda suka yi alla-wadai da hare-haren da Isra’ila take kaiwa.

Danladi ya ce tun lokacin da Isra’ila ta kaddamar da yaki akan yankin na Gaza an kashe dubban Falasɗinawa da yawa daga cikinsu mata ne da ƙananan yara.

Ya kara da cewa asibitoci da makarantu suma basu tsira ba daga luguden wutar Israila.

Ya cigaba da cewa karin goyon baya da Falasɗinawa suke samu daga mutane daban-daban masu banbancin addini ciki harda Yahudawa ya nuna karara cewa Isra’ila ce kasa da aka fi kyara a duniya yanzu a saboda haka ne suke kira ga gwamnatin tarayya da ta yanke duk wata alaka da Isra’ila.

More from this stream

Recomended