Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta bayar da wa’adin kwanaki 15 ga gwamnatin jihar Kano, inda ta bukaci a magance koke-kokensu ko kuma su shiga yajin aikin.
An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taron majalisar gudanarwar jihar, biyo bayan gazawar gwamnati wajen warware batutuwan da aka da su taso a baya a rubuce-rubuce da dama.
A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren kungiyar ta NANNM kuma jami’in hulda da jama’a na jiha, Kwamared Ahmad Hamzat Sharada, wadda kuma aka aika wa shugaban ma’aikatan jihar Kano, kungiyar ta yi gargadin cewa ma’aikatan jinya da ungozumomi a sassan asibitoci da cibiyoyin horo a jihar za su janye ayyukansu. bayan sanarwar ta ƙare ranar 16 ga Oktoba, 2024.
Wasikar ta zayyana muhimman bukatu, da suka hada da biyan kudin alawus alawus na hadari ga ma’aikatan jinya, daidaita tsarin aikinsu, da biyan karin kashi 259% na tsarin albashi na CONHESS.
Ma’aikatan jinya da ungozumomi na Kano sun yi barazanar yajin aikin saboda rashin biya musu bukatu
Date: