Ma’aikatan jihar Nasarawa za su koma yajin aiki kan biyan albashi

Kungiyar Kwadago
Kungiyar kwadago reshen jihar Nasarawa ta zargi gwamnati kan biyan tsohon albashi maimakon sabon

A Najeriya, ma’aikatan gwamnatin jihar Nasarawa sun yanke shawarar ci gaba da yajin aiki har sai yadda hali ya yi, bayan abin da suka kira wata matsala da ta kunno kai a yarjejeniyar da suka kulla tsakanin bangarensu da na gwamnatin jihar.

Ma’aikatan sun bayyana fargaba da rashin amincewa, game da wani sharadi a yarjejeniyar, wanda ya ce gwamnatin jihar za ta iya komawa ga tsarin biyan albashi na da, idan har kason kudin da ta samu daga asusun tarayya bai kai wani adadi da za ta iya sabon tsarin albashin ba.

Sai dai bangaren gwamnatin jihar ya bayyana mamaki game da shawarar da ma’aikatan jihar suka yanke ta ci gaba da yajin aikin.

Bisa ga dukkan alamu dai, har yanzu da sauran rina a kaba, dangane da batun yajin aikin da ma’aikatan jihar Nasarawa suka shiga a makon da ya gabata.

Domin kuwa bayan dage yajin aikin, da kuma cim ma yarjejeniya tsakanin bangaren ma’aikatan da na gwamnatin jihar, yanzu haka ma’aikatan jihar sun yanke shawarar ci gaba da yajin aikin, har sai yadda hali ya yi, bayan daidaita wani bambancin ra’ayin da ya kunno kai daga bangaren wasu ma’aikatan kiwon lafiya.

A cewar Kwamared Yusuf Sarki Iya, shugaban reshen jihar Nasarawar na hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa, wato NLC ya ce dalilin da ya sa za su ci gaba da yajin aiki shi ne: ”Tun da muka tsunduma yajin aiki mun zanta da bangaren gwamnati kan matakan da za a dauka domin cimma matsaya, mun yi yarjejeniya da alkawarin janye yajin aiki idan muka zo rattaba hannu a yarjejeniyar.

Da muka je domin sanya hannu sai muka lura gwamnati kamar sun taba wani bangare na yarjejeniyar da ke nuna idan kudin da gwamnati ke samu daga bangaren tarayya ba su kai Biliyan 4 ba, to ba za abiya ma’aikata sabon mafi kanknatar albashi ba. Don haka za akoma ana biyansu da tsohon tsarin da a ka bari na baya.”

Sai dai bangaren gwamnatin jihar Nasarwar ya yi mamakin jin wannan sabuwar matsaya da ma’aikatan suka cim ma, ta ci gaba da yajin aikin. A cewa Ibrahim Adara, skataren yada labarai na gwamnan jihar:

”Ko kadan wannan zance ba haka ya ke ba, hasalima a zaman da aka yi da gwamna AA Suke shi ne ya janyo hankalinsu akan wannan batu kan cewa idan kudin sun kai haka ko ba su kai ba, yaya za a uyi. wannan bayani shi ne ya taimakawa kungiyar kwadagon suka san da wannan bayani, domin kada sai nan gaba an gama yarjejeniya su ce ba su san magana ba.”

A yau ne dai bangaren kungiyar kwadagon zai sake mika wa bangaren gwamnatin jihar Nasarwar, sabuwar matsayar da ma’aikatan suka cim ma a wajen wani babban taron da suka gudanar a jiya. Don a sake duba bukatun nasu.

More from this stream

Recomended