
Asalin hoton, Getty Images
Luis Suarez ya ci Kofin La Liga hudu a kakar wasa biyar na farko da ya murrza leda a Barcelona
Dan wasan Barcelona Luis Suarez ya amince ya tafi Juventus, a cewar dan jaridar BBC Radio 5 Live Guillem Balague.
Suarez zai tafi Juventus ne ba tare da kungiyar ta biya Barca ko sisi ba – ko kuma ta biya kudi kadan – idan zai iya rarrashin kungiyarsa ta bar shi ya yi gaba.
Dan kasar ta Uruguay yana da ragowar shekara daya a Barcelona a kwangilar da ya sanya hannu a 2016 amma idan ya murza kashi 60 cikin 100 na leda a kakar wasan 2020-21 za a tsawaita zamansa da shekara daya.
Suarez zai yi murna idan aka ba shi alawus na kakar wasa guda.
Kafofin watsa labaran Italiya sun rawaito ranar Juma’a cewa akwai bukatar ya rubuta jarrabawar gwaji ta zama dan kasar kafin a ba shi damar murza leda a can – yana da fasfo na Uruguay kuma ya buga wasa a Sufaniya saboda matarsa tana da fasfo na Italiya, kuma hakan ya wadatar ya zama dan Tarayyar Turai a La Liga.
Tafiyar dan wasan mai shekara 33 Juventsu ba ta da alaka da abin da ke faruwa da abokinsa Lionel Messi.
Suarez da Messi – tare da iyalansu – sun shaku sosai amma matakin da Messi ya dauka kan ko ya zauna ko kuma ya bar Nou Camp ba zai shafi tafityar Suarez ba.
Suarez zai hadu da babban abokin hammayar Messi, wato Cristiano Ronaldo.
Suarez ya koma Barcelona daga Liverpool akan £74m a 2014 kuma ya zura kwallo 198 a wasa 283 da ya buga wa kungiyar.