Loko Yayi Wa Sarki Sanusi II Kauye Da Yawa

Mai martaba sarkin Loko, Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya shaida wa wakiliyarmu Zainab Babaji cewa daga Kano aka kai tsohon sarkin zuwa karamar hukumar Loko inda zai zauna zuwa wani lokaci.

A cewarsa bai san tsawon lokacin da Sarki Sanusi II zai yi a Nasarawa ba, gwamnati ce zata yanke wannan hukuncin.

Ya ce “bai kamata a Kawo Sarki Sanusi nan ba, saboda Loko yayi kauye da yawa. A ganina ba zasu barshi ya dade a nan ba, kafin su canza masa waje.”

Tun Jiya dai ‘yan Najeriya ke ta mayar da martini kan wannan batu da ya sami Sarki Sanusi II, inda da yawansu ke ta kokawa da lamarin, wasu kuma murna suke yi.

Wakiliyarmu Zainab Bababji ta yi kokarin jin ta bakin gwamnnatin Nasarawar amma bata same su ba saboda yanayin dare.

More from this stream

Recomended