Liverpool za ta lashe Premier a karon farko tun bayan shekara 30

Premier league

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Liverpool za ta ci gaba da sa kaimi na lashe kofin Premier bana, inda za ta kara da Everton ranar 21 ga watan Yuni da zarar an ci gaba da gasar 2019-20 ba ‘yan kallo.

Wannan ne karon farko da Liverpool za ta ci kofin Premier League tun bayan shekara 30. Shin a wane wasan ne za ta dauki kofin bana?

Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da wasannin Premier League na shekarar nan da kwantan wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal.

Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin tamaula a Ingila sakamakon bullar cutar korona, daga baya kungiyoyin da ke buga gasar Premier suka amince za su karkare kakar 2019-20.

Liverpool tana ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City, kuma wasa biyu za ta ci a ba ta kofin bana a karon farko tun bayan shekara 30.

Sai dai kuma Liverpool din za ta iya cin kofin da zarar Arsenal ta doke Manchester City ita kuma kungiyar ta Anfield ta yi nasara a kan Everton.

Wasu kwanakin da ake ganin za a bai wa Liverpool kofin Premier na shekarar nan sun hada da ranar 24 ga watan Yuni lokacin da za ta karbi bakuncin Crystal Palace ko kuma 2 ga watan Yuli a wasa da Manchester City.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya ci kwallo 16 a kakar bana yana kan-kan-kan da Sergio Aguero na Manchester City a mataki na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier bana.

Dan kwallon Leicester City, Jamie Vardy shi ne kan gaba da kwallo 19 a raga sai kuma dan wasa Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang mai 17 a raga.

Ranar ta 19 ga watan Yuni Tottenham wadda take da takwas a teburin Premier za ta karbi bakuncin Manchester United, ita kuwa Leicester City wadda take ta uku za ta ziyarci Watford ranar 20 ga watan Yuni.

A dai ranar ta Asabar da za a ci gaba da wasanni Arsenal za ta je Brighton and Hove Albion, yayin da Aston Villa za ta kece raini da Chelsea ta hudu a teburi ranar 20 ga watan Yuni.

Manchester City za ta kara wasa ranar Litinin 21 ga watan nan, inda za ta yi wa Burnley masauki.

Za a nuna wasannin da za a ci gaba da gasar Premier League a talabijin wadda za a fafata ba ‘yan kallo don gudun yada cutar korona.

Jadawalin wasannin Premier League da za a ci gaba:

Laraba 17 ga watan Yuni kwantan wasanni

 • Aston Villa da Sheffield United
 • Manchester City da Arsenal

Juma’a 19 ga watan Yuni

 • Norwich City da Southampton
 • Tottenham Hotspur da Manchester United

Asabar 20 ga watan Yuni

 • Watford da Leicester City
 • Brighton & Hove Albion da Arsenal
 • West Ham United da Wolverhampton Wanderers
 • Bournemouth da Crystal Palace

Lahadi 21 ga watan Yuni

 • Newcastle United da Sheffield United
 • Aston Villa da Chelsea
 • Everton da Liverpool

Litinin 22 ga watan Yuni

 • Manchester City da Burnley

Talata 23 ga watan Yuni

 • Leicester City da Brighton & Hove Albion
 • Tottenham da West Ham United

Laraba 24 ga watan Yuni

 • Manchester United da Sheffield United
 • Newcastle United da Aston Villa
 • Norwich City da Everton
 • Wolverhampton Wanderers da Bournemouth
 • Liverpool da Crystal Palace

Alhamis 25 ga watan Yuni

 • Burnley da Watford
 • Southampton da Arsenal
 • Chelsea da Manchester City

Asabar 27 ga watan Yuni

 • Aston Villa da Wolverhampton Wanderers

Lahadi 28 ga watan Yuni

Litinin 28 ga watan Yuni

 • Crystal Palace da Burnley

Talata 30 ga watan Yuni

 • Brighton & Hove Albion da Manchester United

Laraba 1 ga watan Yuli

 • Arsenal da Norwich City
 • Bournemouth da Newcastle United
 • Everton da Leicester City
 • West Ham United da Chelsea

Alhamis 2 ga watan Yuli

 • Sheffield United da Tottenham Hotspur
 • Manchester City da Liverpool

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...