Shugaban Bayern Munich Uli Hoeness ya ba da tabbacin cewa kungiyarsa na neman dan wasan Manchester City, Leroy Sane, a cewar (Suddeutsche Zeitung – in German).
Arsenal za ta fara neman dan wasan Scotland, Ryan Fraser, mai shekara 25, bayan sun buga wasan karshe a Gasar Europa, sai dai ita ma Bournemouth ta taya dan kwallon a kan fam miliyan 30, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.
Tottenham ta fara magana da Real Madrid don fara yunkurin mallakar dan wasan Spain, Marco Asensio, mai shekara 23, sai dai Madrid ta ce mata dan kwallon ba na sayarwa ba ne, in ji (AS – in Spanish).
Manchester United tana ci gaba da zawarcin dan wasan Faransa, Adrien Rabiot, wanda yake shirin barin kungiyarsa ta Paris St-Germain a kakar bana, a cewar (Manchester Evening News).
Har ila yau, United ta ce za ta kara wa dan wasan Ajax, Matthijs de Ligt, kudi bayan ta fara taya shi a kan fam miliyan 12 a tsawon shekara daya, in ji (Sport, via Express).
Kocin Newcastle Rafael Benitez ya shaida wa Marseille da Roma cewa zai ci gaba da zama a kungiyarsa kuma tayin da suka yi masa su kai kasuwa, in ji Chronicle.