HomeHausaLionel Messi: Shin wannan ne ƙarshen rayuwar Messi a Barcelona?

Lionel Messi: Shin wannan ne ƙarshen rayuwar Messi a Barcelona?

Published on

spot_img
Messi

Asalin hoton, Getty Images

Sanarwar da Barcelona ta fitar a yammacin Alhamis ta girgiza duniyar ƙwallon ƙafa.

Wannan na zuwa ne yayin da fitaccen ɗan wasan na Argentina mai shekara 34, wanda ba shi da yarjejeniya tun 1 ga watan Yuli, ke fatan sabunta yarjejeniya domin tsawaita zamansa na shekara 21 a Barcelona.

Barcelona ta ce a ranar Alhamis ya kamata Messi ya sa hannu kan yarjejeniyar, amma aka samu cikas ga dokoki da sharuɗan kuɗi na hukumomin La Liga.

Yanzu mece ce makomar ɗan wasan da ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya sau shida? Shin wannan ne ƙarshen rayuwarsa a Barcelona, ko akwai wata mafita a ƙarshe?

Me ya sa yarjejeniyar ta gagara?

A farkon wannan watan, mai sharhin ƙwallon ƙafa a Sifaniya Guillem Balague ya ruwaito cewa Messi ya amince ya ƙulla sabuwar yarjejeniya har zuwa 2026 inda ya amince a datse rabin albashinsa.

Amma kuma dole sai Barcelona ta sayar da wasu ƴan wasanta domin ta samu kuɗin riƙe Messi – wato ta rage kuɗin da take kashewa ga biyan albashi da kusan yuro miliyan 200 domin cimma ka’idojin La Liga na ƙashe kuɗi – amma hakan ya gagara.

Har yanzu Antoine Griezmann da Ousmane Dembele da Philippe Coutinho – da sauransu – har yanzu suna Barcelona.

A lokacin da yake tsokaci a shirin sharhin ƙwallon ƙafa na BBC Radio 5, Balague ya ce: “Barca ta yi ƙoƙarin samo hanyoyin da za ta iya biyan albashin Messi da alawus dinsa, kuma na tambaye su, ‘ta yaya za ku cimma haka tun da kun kasa rijistar sabbin ƴan wasa’? amsar da suka bayar ita ce ‘kawai ka yarda da mu.’

“Saƙon da ya fito daga ɓangaren Messi shi ne, a jira.” Laporta (shugaban Barcelona) yana da kyakkyawan fata, saɓanin ɓangaren Messi. Kuma babu wani lokaci guda da aka nuna cewa hakan ba zai yiwu ba.

“Yanzu kuma an tabbatar da cewa babu wata hanyar da za a iya tabbatar da yiwuwar hakan. Amma ko wannan zai iya zama ƙarshen labarin.”

Ernest Macia na Rediyo Catalunya ya shaida wa BBC cewa: “mutane da dama na mamakin yadda rayuwa za ta kasance babu Messi saboda babu wanda ya taɓa tunanin hakan a cikin waɗannan kwanaki uku.

“Mun ji wasu maganganu a ƙungiyar, shi kansa shugaban Barca Joan Laporta yana cewa Messi zai zauna. An tanadi yarjejeniya da za a ƙulla an riga an rubuta.

“A cikin sanarwar kamar Barcelona da Messi sun amince – sun fahimci juna. Maimakon haka halin matsalar kuɗi da ƙungiyar ke ci, da kuma sharuɗɗan La Liga… amma muhimmin batun shi ne cimma sharuɗɗan hukumomin La Liga.

Shin wannan wasa ne?

Tsokacin Andy West mai sharhin ƙwallon ƙafa a Sifaniya

Ba lokaci ne na aika saƙwannin yin bankwana ba, kamar yadda wasu suke gani, domin sanarwar Barca ba ya nufin Messi zai tafi, da saura.

Watakila wata dabara ce ta barazana da wasa da hankalin La Liga, wadda sharuɗɗanta suka hana Messi da Barca ƙulla sabuwar yarjejeniya da suke iƙirarin cimma.

Tushen matsalar kuɗin Barcelona na da alaƙa da ra’ayinta na shirin kafa gasar Super League na manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai inda shugaban ƙungiyar Joan Laporta ke ci gaba fafutika tare da takwaransa na Real Madrid Florentino Perez.

Abu mai muhimmanci shi ne sanarwar ƙulla yarjejeniya da La Liga ta yi da kamfanin saka jari na CVC, wanda nan take Barca ta samu kusan fan miliyan 200 – kuɗin da ya isa ta sake ƙulla yarjejeniya da Messi.

Domin samun kudin, sai ƙungiyar ta jaddada amincinta da La Liga, tare da janye matakin kafa Super League.

Laporta ya faɗa wa shugaban La Liga Javier Tebas cewa: “Bari mu ga shirin da sabon kamfanin abokin huldarka zai yi da La Liga ba tare da Messi ba.

Me zai kasance makomar wannan matakin… wa ya sani?

Me zai kasance yanzu makomar Messi?

Ba a daɗe ba da Messi ya ce yana son yarjejeniyarsa ta ƙunshi damar ficewa a lokacin da yake so, amma Barca ta ce dole sai an biya yuro miliyan 700.

Yanzu babu wannan sharaɗin.

An daɗe ana alaƙanta shi da tsohon mai horar da shi Pep Guardiola na Manchester City.

Bayanan bidiyo,
Shin Messi zai koma Man City ne?

Amma City da ta saye Jack Grealish kan fan miliyan 100 tana kuma farautar ɗan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, Balague na ganin City da wuya ta iya ɗaukar Messi bisa sharuɗɗan dokar adadin kuɗin sayen ƴan wasa.

“Bisa wannan ban yi tunanin City tana da kudin sayen Messi ba, amma mun fi ganin Paris St-Germain ta latsa.”

Babban mai sharhin ƙwallon ƙafa a Faransa Julien Laurens ya ce a bara PSG ta ce idan Messi yana ra’ayinta tana da kudin da za ta iya sayensa.

(BBCHausa)

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...