Lionel Messi: Bai kamata a biya euro 700m ba kafin Messi ya bar Barcelona, in ji mahaifinsa

Lionel Messi

Bayanan hoto,
Messi ya shafe sana’ar kwallon kafarsa a Barcelona

Mahaifin Lionel Messi wanda kuma shi ne wakilinsa ya shaida wa La Liga cewa bai kamata a biya euro 700m (£624m) kafin dan wasan na Barcelona ya bar kungiyar.

A makon jiya ne dan wasan mai shekara 33 ya shaida wa kungiyar cewa yana so ya yi gaba bayan shekara 20 yana murza mata leda kuma ya yi amannar cewa zai bar kungiyar ba tare da biyan ko sisi ba.

Sai dai Liga ya yi raddi inda ta ce dole ya biya kudin kafin ta bar shi ya tafi wata kungiyar.

Kungiyar ta Sufaniya ta ce: “La Liga ta yi raddi kan sakon da ta samu daga daga wakilin Leo Messi.

“A cikin raddin, La Liga tana mai cewa su yi wa kwangilar bahaguwar fahimta. La Liga tana nanata sanarwar da ta wallafa ranar 30 ga watan Agusta.”

More from this stream

Recomended